Mgbidi
Mgbidi | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Imo | |||
Yawan mutane | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | |||
Labarin ƙasa | ||||
Bangare na | Oru ta Yamma |
Mgbidi Ita ce hedikwatar Oru West, ƙaramar hukumar jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya. Garin na a yankin latitude 5.37° N da longitude 6.57° E. Kuma nan ne hedikwatar ƙaramar hukumar Oru kafin a raba garin zuwa ƙananan hukumomi biyu, Oru West da Oru East, a 1996 ƙarƙashin shugabancin Sani Abacha.
Wuri da iyakoki
[gyara sashe | gyara masomin]Mgbidi na ɗaya daga cikin tsofaffin garuruwa a jihar Imo. A arewa tana da iyaka da Ibi-Asoegbe da Aji, daga gabas ta yi iyaka da Amiri da Otulu, daga yamma kuma tana da iyaka da Ozara, a kudu kuma tana da iyaka da ƙaramar hukumar Oguta da Awo-omamma. Mgbidi na da nisa sosai daga arewa a jihar Imo, shi ya sa, ya ke da iyaka da Amorka a ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra. Kogin Awbana ya samo asali ne daga Mgbidi kuma ya malala zuwa tafkin Oguta, ya zama ɗaya daga cikin magudanan ruwa.
Al'umma masu cin gashin kansu
[gyara sashe | gyara masomin]Mgbidi yana da al'ummomi goma sha ɗaya, waɗanda aka haɗa su don kafa ƙungiyoyi masu cin gashin kansu guda shida da aka samu a Mgbidi. Al’ummomin goma sha daya sune Imeoha, Eziali, Umuekwe, Okwudor, Umuorji, Umuokpara, Umueshi, Umuabiahu, Uzinaumu, Ihitte da Ugbele. 5°44′9″N 6°53′0″E / 5.73583°N 6.88333°E